An kashe masu makoki a Syria

Masu zanga zanga a Syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga zanga a Syria

Rahotanni daga Syria sun ce jami'an tsaro sun bude wuta tare da kashe masu makoki akalla guda sha daya, wadanda ke halartar masu zanga-zangar da jami'an tsaro suka harbe a jiya.

An kuma ba da rahoton jin harbi a kewayen Dimashque, babban birnin kasar, da garin Homs na yamma da kuma Izraa a kudu.

Sai dai wata mata a birnin na Damascus, wadda ke goyon bayan gwamnati ta dora ma masu zanga-zanga da aka kashe a jiya laifi, inda tace wadanda aka kashen an kashe su ne saboda suna dauke da makamai.

An kuma ba da rahoton wani 'yan majalisar Syriar su biyu sun yi murabus bisa kisan mutane fiye da saba'in da jami'an tsaro suka yi a jiya.