Shugaban Yemen zai sauka daga mukaminsa

Masu gudanar da zanga-zanga a Yemen Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Yemen zai sauka daga mukaminsa

Jam'iyyar da ke mulki a Yemen ta amince da wani shirin kungiyar kasashen larabawa da ya tanadi shugaba Ali Abdallah Saleh ya sauka daga kan mulki.

Sai dai shirin ya tanadi yanayin da zai sa shugaban ya samu kariya daga fuskantar tuhuma.

Ana sa ran wannan shiri zai kawo karshen boren da ake yi a kasar.

Shugaba Ali Saleh zai mika ragamar mulki ne ga mataimakinsa cikin kwanaki talatin da ke tafe.

Sai dai kuma ba haka yawancin 'yan kasar ta Yemen suka so ba.

Yawancin 'yan kasar dai, musamman matasan da ke bore akan tituna, sun fi so ne Shugaba Ali Abdallah Saleh ya sauka daga kan mulki nan take.