Wasika ga shugaba Goodluck

Wasu kungiyoyin kare hakkin Bil Adama a Najeriya na nuna damuwa a bisa abinda suka ce ci gaba da take hakkin Bil Adama da jamian tsaro ke yi a wuraren da aka sami rikicin addini dana kabilanci, bayan zaben shugaban kasa da akayi a Najeriya.

Kungiyar Civil Rights Congress wato CRC na cikin kungiyoyin dake nuna irin wannan damuwa.

Kan haka ne kuma ya kungiyar ta rubuta wata wasika ga shugaban Najeriya Goodluck Jonathan,inda ta bukace shi da ya dakatar da dabi'un take hakkin Biladama da jamian tsaro ke yi a wuraren da aka yi zanga zangar adawa da sakamakon zaben shugaban kasar daya baiwa shugaba Jonathan din nasara.