Kuwait zata tallafawa 'yan tawayen Libya

Wani jagoran 'yan tawayen kasar ta Libya ya ce kasar Kuwait ta yi masu alkawarin za ta ba su kudi Dala milyan dari da tamanin a matsayin agaji, yayin da suke ci gaba da fafatawa da dakaarun gwamnatin Libya.

Jagoran Majalisar Wucingadi ta Kasar Libyar, Mustafa Abduljalil, ya ce 'yan tawayen suna bukatar kudi ruwa a jallo, wanda zai taimaka wajen biyan albashi.

Ministan harkokin wajen Kuwai ya sheda ma manema labarai cewa agajin jin kai ne na gaggawa.