An harbe wani dan Isra'ila a Nablus

An harbe har lahira wani dan Isra'ila tare da raunata wasu akalla hudu, a kushewar Annabi Yusuf Alaihis Salaam a birnin Nablus na yankin Falasdinawa.

Wata jaridar Israila ta ce wanda aka kashe, Ben Yosef livnat, ministan al'adu na Isra'ilar, Limor Livnat, kawunsa ne.

Wani wakili a Kwamitin Zartarwa na Kungiyar PLO mai neman 'yancin Falasdinawa, Saeb Erekat, ya zargi halyayyar 'yan kama-wuri-zaunan da jawo taho-mu-gamar.

Inda yace wani gugun 'yan kama-wuri-zauna ne ya kutsa kai kushewar Annabi Yusuf, Alaihis Salaam, ba tare da shedawa jami'ai ba don a samar da tsaro.

Kuma bisa ka'ida abinda ya kamata su yi kenan amma ba su yi ba.