Paparoma ya yi addu'ar zaman lafiya a Afirka

Paparoma Benedict ya yi kiran samun tattaunawa da kuma difilomasiya a kan rikicin Libya.

Haka kuma ya yi kiran a kai kayan agaji ga wadanda ke bukata.

Paparoman ya yi fatan samun hadin kai da aiki tare a tsakanin matasa a arewacin Afrika, domin daukaka ayyuka masu alfanu ga jama'a, su kuma gina al'ummar da ta yi nasara a kan talauci.

Paparoman yana jawabi ne a Dandalin St Peter a fadar Vatican, a matsayin wani bangare na bukin Ista.