Lallai ne shugaban Yemen ya sauka

Shugaban kasar Yemen Ali Abdallah Saleh Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban kasar Yemen Ali Abdallah Saleh

Dubun-dubatar masu zanga-zangar kyamar Shugabancin Abdullah Saleh a Sanaa, babban birnin Yemen, sun tsaya kan bakansu na ganin lalle shugaban ya sauka yanzu.

Sai dai kuma shugaban wanda ya amince ya mika mulki domin a bashi kariya daga tuhuma ya yi gargadin cewa zanga zangar kyamar gwamnatin da ake zatai mummunar illa ga kasar.

Shugaba Ali Abdullahi Saleh ya ce akwai 'yan alqaeda a cikin masu adawa da gwamnati ya kuma yi gargadin cewa kasashen kasashen yammaci zasu dandana kudarsu.

Sai dai kuma masu zanga zangar sun musanta wata alaka da kungiyar alqaeda.