Fursunoni sun gudu daga kurkukun Kandahar

Taswirar Afghanistan Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Fursunoni sun gudu daga gidan yarin Kandahar

Fursunoni da dama ne suka tsere daga babban gidan yarin birnin Kandahar da ke kasar Afghanistan.

Daruruwan masu zaman gidan kason dai sun gudu, kuma wani ma'aikacin gidan yarin ya ce, lamarin ya auku ne ta hanyar amfani da wata hanya da aka tona ta kasa.

Nan take dai aka kama wasu 'yan fursunan da suka yi kokarin tserewa.

A baya dai kungiyar Taliban takan shirya balle gidan yarin na birnin Kandahar da karfin tsiya da nufin kubutar da wasu 'yan fursuna.