Zaben gwamnoni da 'yan majalisun jihohi

Image caption An yi zaben gwamnoni ne a jihohi 24 a Najeriya

19:04 A yanzu haka mun kawo karshen bayanan da muke kawo muku kai tsaye a wannan shafin. Har wa yau zamu kawo muku sakamakon zabukan idan hukumar zabe ta bayyana su. Sai ku kasance da shirye-shiryen mu ta rediyo domin samun karin bayani.

18:59 An kammala zabukan gwamnoni da 'yan majalisu a yayinda ake ci gaba da kidaya kuri'u a mazabu.

18:36 Kabs Daura BBC Hausa Facebook: Ina ga lokaci yazo da mu 'yan Nigeria zamu tashi mu fadakar da wadanda suka cucemu suka saida kuri'ar su don rashin sanin 'yan cinsu, muyi himma wajen fadakar da su, mu roki Allah ya mana jagora amin.

18:16 A yanzu mungama jefa kuri, ana kirgawa sojoji sunzo sun koremu yanzu ba batun tsarewa balle rakawa. Daga Aminu Abdu Baka Noma Sani Mai Nagge Kano.

17:55 A kusan dukkan mazabun dake a katsina an kammala zabe lafiya, sai dai akwai tsananin zargin aikata laifuffukan zabe, wadanda suka hada da satar akwati da amfani da yan bangar siyasa. Daga Muhd Sayyadi Jibia.

17: 40 Bidiyon zaben gwamna da 'yan majalisua jihar Nassarawa. http://www.bbc.co.uk/hausa/multimedia/2011/04/110426_gov_election.shtml

17:38 Hotunan zaben gwamnoni da 'yan majalisu a wasu sassan Najeriya. http://www.bbc.co.uk/hausa/multimedia/2011/04/110425_niggove_gallery.shtml

17:33 Anan karamar hukumar Ebeno a jihar Akwaibom, zabe na tafiya cikin kwanciyar hankali. Daga Aminu Danjuma.

17:16 Mudai a garin Potiskum namu zabe yana tafiya lafiya sai dai muce Allah yamana jagora mafi Alkairi. Daga Saleh Lawal

17:11 An kamala kada kuri'a a mazabar unguwar Rimi cikin garin Tangaza a jahar Sokoto sakamakon rashin fitowar jama'a wajen zabe. Daga Umar Garba.

17:03 A mazabar kwado Hajj camp Katsina, wakilan wata jam'iyya sai sayen kuri'a suke yi, bayan sun kwana raba kudi da atamfa da kuma sabulu a unguwar jiya. Idan ka dangwala musu sai ka daga wakilinsu ya shedaka. Wannan zaben bai yi ko kusa da inganci ba. Daga Engr. A B Kassim.

16:53 Yaushe talakan Najeriya zai gane 'yancinsa, adaina amfani da shi wuri satar akwatin zabe. Daga Ado Isa Daura.

16:50 Jama'a kuyi hakuri ku fito ku kada zabe don a kawar da gwannatoci marasa adalci a Nigeria. Daga Muhammad M Baba Afoto Gamawa Bauchi.

16:47 Gyaran zaben Najeriya fa sai dai Allah, saboda har yanzu akwai shi da gyara. Daga Hassan Mai Waya Shago Goma Kangiwa.

16:44 Zabe a jalingo na gudana cikin kwanciyan hankali to amma ba a fito ba kamar yadda ye kamata. Daga Zaharadeen Muhammed.

16:42 Nidai tuni nayi zabe a mazabar Gajida kuma abubuwa na tafiya kamar yadda yakata saidai yan abubuwan da ba'a rasaba. Daga Balarabe Yusif Babale Gajida.

15:47 Garba Jibrin BBC Hausa Facebook: Mu dai anan karamar hukumar Mallam Madori jihar Jigawa jama'a basu fito ba sosai.

15:46 Kabiru Sakaina BBC Hausa Facebook: Babbar matsala a zaben yau itace rashin fitowar jama'a. Gaskiya abin ba dadi.

15:44 Jazuli Baba Sadi daga Jalingo: Na kada kuri'a a rumfar zabe, amma a gaskiya jama'a basu fito sosai ba.

15:43 Naziru Daura BBC Hausa Facebook: Da'alama talakawa mun amsa kira yadda yakamata, domin idan ka zagaya kowace rumfa a garin Daura, jama'a ne suka fito `kwansu da kwar kata don kada kuri'a. Allah ya bamu nasara.

15:41 Saleh Muhd Tahir BBC Hausa Facebook:Mu dai a nan garin Kirenowa mutane ba su fito sosai ba domin duk rumfunan zabe guda shida na cikin gari ba jama'a sosai.

15:38 Adamu Yusuf Yero Gombe BBC Hausa Facebook: Mu dai a mazabar mu dake dawaki 006 a jihar Gombe, muna nan muna ta kada kuria amma kash! mutane ransu ya baci basu fito zabe ba, wa su kuma sun ji tsoron fitowa. Allah ka samar mana da mafita.

15:35 Wannan dama ce garemu mutanen Nigeria wadda idan ta wuce ba zamu sake riskarta ba sai shekaru hudu masu zuwa dan haka mu fito kwanmu da kwarkwata mu kada kuri'armu,sannan kar mu yadda da wadanda zasu bamu kudi domin mu sayar musu da yancin mu KUKAN KURCIYA JAWABI NE. Daga Sani Muhammad mazabar Fagge.

15:28 Rahotanni daga sassa dabam-daban na jihar Katsina na nuni da cewa zaban na yau ya fuskanci matsaloli, kama daga satar akwatunan zaben, da kwace kayan zaben ma gaba daya a gudu da su. Wasu wuraren a birane inda aka kai akwatunan akwai bayanan da ke nuna 'yan banga sun rika tada hatsaniya suna dagula zaben.

15:20 Muna yiwa 'yan Najeriya fatan Allah yasa ayi zabe lafiya, Amin: Sako daga Usman Muktar `dan Niger wanda ke kasuwan barchi kaduna.

15:19 Mu dai Talakawa mun `ki zuwa zabe ne don mun san ba zata sake zane ba. Daga Usman Taura a Lagos.

15:18 Mu dai a mazabar mu ta unguwar Kabo a Yawuri babu matsala mun fito mun kada kuri'un mu: Daga Malam Umaru Kamba Yawuri.

15:17 To hukumar zabe mu dai a jihar sakkwato mun fito mun zabi abin da muke so, saura ki tabbatar mana da, abin da muka zaba. Daga Ahmed Ladan Girkau a jihar Sokoto.

15:16 Kai ! mu sai dai mu ce Allah ya zabar mana da abin da yafi alkhairi, domin a mazabar mu an yi `barin Nairori don sayen kuri'u. Daga Hashimu Karami Daudawa Faskari Jihar Katsina.

15:12 Shamaki Ubale Gashuwa jihar Yobe: Mu dai mun fito zabe kuma zamu kasa, mu tsare, mu raka, kuma mu jira, har sai an tabbatar mana da gwamna da 'yan Majalisun da muka zaba.

15:11 A. D. Garba jihar Gombe ya aiko mana da sako ta wayar salula inda yake cewa: Mu kam a jihar Gombe mutane sun yi zaman su a gida, sun `ki ma fita a tantance su ballantana su yi zabe.

14:36 Ina kira ga yan uwana matasa da kudena karbar kudi kuna dangwalawa wanda bashi ku ke ra'ayi ba kuma koni ambani kudi naira 200 nace bazan sayar da yanci na da mutunci na ba. Daga Dahiru Dogon Tela jihar Katsina.

14:32 Wakilin BBC Abdul Isa: A jihar River an kama mutane shida da zargin satar akwatunan zabe, yayinda aka samu tashin hankali a jihar Akwa Ibom wanda yayi sanadiyyar kone-konen motoci.

14:31 Rahotanni daga yankin kudu maso kudancin Najeriya na nuni da cewa, an samu tashe-tashen hakula wasu jihohin yankin yayinda ake gudanar da zabukan gwamnoni da na 'yan majalisar jihohi a yankin.

14:29 Yanzu haka haka harkokin zaben 'yan takarar gwauna da na 'yan majalisar dokokin jihar Lagos na gudana cikin kwanciyar hankali. Zaben a shiyyar kudu maso yammacin Najeriya zai zama wani da dukkan alamu 'yan takarar da suka fito daga jihohin yankin Lagos, Oyo, Ogun suna da karfin fafatawa da takwarorin su.

14:25 Wakilin BBC Haruna Shehu Tangaza: Kodayake dai rumfunan zabe sun bude da wuri kuma akwai kyakkyan tsarin tsaro anan Birnin Kebbi babban abin da kowa ke Magana akai gameda wannan zaben shine rashin fitowar masu zabe a wannan karon.

14:23 Na mika ra,ayina akan manyanmu wanda suka fadi a siyasar da akayi Allah yaba su hakuri da zaman lafiya . Daga Abdulhadi Muhammad Sani a Jigawa kafin hausa.

13:18 A gaskiya mudai mutane sundan fito amma bada yawaba. Sai dai ana amfani da kudi wajan siyar kuria. Daga Babangida Gashua.

14: 11 Wakilin BBC Ishaq Khalid: A jihar Filato a galibin wurare ma'aikatan zabe sun halarci rumfunan zabe da wuri kuma aikin tantancewa masu jefa kuria ya gudana cikin tsanaki inda wadanda aka tantance su kan je gida kafin daga bisani su dawo domin jefa kuri'a.

14:09 A jihohin Filato da Gombe ma dai zabukan na gwamnoni da na 'yan majalisun dokokin na gudana ne cikin matsalloli daban-daban kama daga rashin fitowar jama'a yadda ya kamata da kuma soma jefa kuri'a tun lokaci bai yi ba.

14:05 Gaskiya akwai karancin jama'a a wannan zaben domin acikin kashi dari bai fi kashi ashirin zuwa ashirin da biyar ba wanda suka fito a mazabata ta Babban giji (hausawa) karamar hukumar Tarauni Kano kuma kusan haka ne a sauran mazabu na cikin gari. Daga Nazifi Zubairu.

14:03 Talakawa sunki fitowa su kada kuri'a,in wani ya sami nasara sai suce anyi magudi.mu canza shawara talakawa. Daga Mansoor Said PRP,KANO.

14:01 Zabben yau dai a adamawa babu jamaa ko ina ka za gaya. Daga Bellon Kulu Dubeli Jimeta Yola a jihar Adamawa.

13:55 Wakilin BBC Aliyu Abdullahi Tanko a jihar Neja: Ana sayen kuri'a a wata rumfar zabe dake unguwar Gabas kusa da masallacin Juma'a na Minna.

13:45 Talakawan Kasata Najeriya, yadda Allah Ya kawo mu ranar zaben nan lafiya Allah Ya nuna mana karshensa lafiya. Daga Abdul.

13:36 Yaku talakawan Najeriya kada 'yan kudin da za a baku susa kumanta da wahalar dakuka sha shekarun da suka wuce. Daga Ibrahim Aliyu a jihar Zamfara.

13:18 Malam-Muhd Alkasim Nadabo BBC Hausa Facebook: Mutanen Jihar Katsina, suna ta sayar da kuri'unsu, ta hanyar amsar shadda ko atamfar naira dari takwas da kuma dari biyu kudin dinki. Hmmm, jiki magayi inji 'yan magana. Duk dai wanda ya sayar da yancinshi, zai ci gaba da zama cikin kunci, fatara da talauci. Allah yasa talaka ya gane, ya canza daga wannan halin banzan.

13:15 Ahmed Buba BBC Hausa Facebook: Rashin fitowa zabe, zaiyi illa sosai, don kuwa kowa yasan irin tasirin da gwamnoni suke da shi wajen siyasar Nigeria! Canji yana farawa ne daga zaben gwamna, don cimma burin shekaru hudu masu zuwa.

13:12 Allah yasa wannan zaben gomnonin da na 'yan majalisun jihohi a gudanar da shi cikin lafiya da kwanciyar hankali. Ku kuma jama'a sai ku zabi shugabanni nagari masu adalci da himmar kawo ci gaba kuma masu kishin yankinsu. Daga Muhammad M Baba Aeoto Gamawa Bauchi.

13:06 Shugabanni suyi aiki da gaskiya da rikon amana ba bambanc., Talakawa su dauki hakuri da juriya da amana da yarda da hukuncin ubangiji koda bai musu dadiba. Daga Abubakar Yaroro Hadejia.

12:58 An fara zabe a mazabarmu ta Atafi dake Hadejia jihar Jigawa, amma mutane dayawa basu fito domin kada kuri'arsu ba. Daga Ibraheem Atafi.

12:53 An fara kada kuri'a a yankin funtua, amma mutane basu fito ba sosai. Daga Mainasara Nasarawa Funtua.

12:47 Wuyar aiki ba a fara ba. Mu dai fatan da muke yi Allah yasa aba talakawa abin da suka zaba. Daga Sade Saidu Daura.

12:44 Kabiru Bala Jalingo BBC Hausa Facebook: Alhamdulillah naje nayi zaben Gwamna wadda nake so ALLAH bashi nasara a jihar Taraba.

12:41 Zaben yau kam gaskiya mutane sun fito ne kawai dan tallar katin zaben su kamar nan Gusau. Daga Aminu Maizuma jihar Zamfara.

12:39 A shatale talan wafa inda ake canjin kudi a jihar Kano sojoji sunanan suna buncikar mutane musu ababan hawa idan bakada rijista sai sun saka kayi tsallan kwado wannan abu yayi dai dai. Daga Abubakar Dan Yobe a jihar Kano.

12:37 Yadda zabe ke gudana a yankinmu a jihar Katsina cikin karamar hukumar Katsina Kangiwa ward, Malaman zabe sun fito da wuri sai dai mutane basu fito sosai ba yazuwa yanzu akwai rumfa Kangiwa ward mai kimanin mutane 800 da sukayi ragista amma mutane 160 aka tantance. Daga Sada Tanimu Makeri Saulawa Katsina.

12:33 Mu kam a nan Zamfara mutane sun fito sai dai akwai banbanci da zabukan da suka gabata. Daga Yusuf naka girmanka

12:30 Anan garin kazaure dan Allah ina kira ga 'yan uwana talakawa dasu fito yin zaben yau shine zai sa kasarmu ta ci gaba kuma an gama tantancewa yanzu ana jiran lokaci yayi domin fara zaben na yau Allah yasa mudace da shuwagabanni na gari Amin. Tijjani Kazaure.

12:22 Abdul Arab daga Uromi jahar Edo: Mu dai a mazabar mu na wolfayif har zuwa karfe 12.00 rana mutane goma sha biyu ne kawai suka fito Allah yasa ayi zabe lafiya.

12:18 A jihar Kogi ma, rahotanni sun nuna cewa mutane ba su fito sosai ba.

12:17 A jihar Neja dai, baya ga zaben na gwamna da 'yan majlisar jiha ana kuma gudanar da zaben majalisar tarayya a shiyyar arewacin jihar.

12:16 A wasu wuraren ma a jihar Neja ma'aikatan zabe da jami'an tsaro ne ke dakon masu kada kuri'a. Sai dai komai na gudana lami lafiya.

12:14 Sabanin yadda jama'a suka yi tururuwa don kada kuri'a a lokacin shugaban kasa, a zaben gwamna da 'yan majalisar jiha, jama'a kadan ne suka fito a jihar Neja.

12:06 Na fito wurin tantancewa tun 6:30, amma na tarar da mutane sun fi tamanin a gabana. PU012. Kankarofi ward Kano municipal. Daga Maifada Kamilu Bashir.

12:04 Fatana shine mu 'yan Najeriya Allah sa kasarmu ta zauna lafiya kuma da fatan shugabanninmu zasu sa Allah a ransu wajen mulkin talakawa. Daga Sani Kazaure.

12:00 Lokacin kada kuri'a shine lokacin da ake gane yawan jama'ar da suka fito zabe, saboda a lokacin ne kowa ke fitowa domin hawan layin kada kuri'a bayan tantacewa da aka yi, a mafi yawancin mazabu yanzu haka an fara jefa kuri'a, sai dai layuyyukan ba yabo sai dai fallasa, saboda a kusan ko wace rumfa da kyar ka samu rabin masu rijista a rumfar sun fito domin yin zaben. Daga Muh'd Sayyadi Filin-Sale, Jibia, Katsina.

11:52 A Jihar Enugu da Anambra da ke kudu maso yammacin Najriya, rahotanni sun nuna cewa mutane ba su fito sosai ba. Sai dai a Jihar Anambra ba a zaben gwamna sai na 'yan majalisun jihohi.

11:51 Mutane sun zauna abun su a gida, sun ki fitowa a tantance su. Ina ganin haka yana da nasaba da abunda ya faru na zaben shugaban kasa. Daga Abubakar Aliyu, jihar Neja.

11:41 A gaskiya mu dai al'amarin zabe na tafiya dai dai halin yanzu domin kuwa an tantance mu harma an fara kada kuri'a. Daga Ibrahim Abdulrazaq, Panshekara Kano.

11:35 Ma'aikatan zabe masu yi wa kasa hidima sun kauracewa wuraren aikinsu yayin da dubban mutanen da ke gudun hijira ba za su samu damar kada kuri'a a zaben gwamnoni da 'yan majalisar johohin da ake gudanar wa.

11:32 Yanzu haka a mazabata, naga ankawo akwatin zabe da ink da kuma ballot paper, kuma tuni jama'a sun hau layin zabe a mazabata dake Galadanchi. Daga Zainab

11.20 Talakan Najeriya ya kara hakuri kan abinda ya faru a kan zaben shugaban kasa, ya fito don zaben gwamnoni da 'yan majalisu. Ya kasa ya tsare ya raka ya jira. Daga Murtala Saliu a Kano.

11:18 Abdullahi Mahmud BBC Hausa Facebook: A yanzu gamu nan muna zaune muna jiran mutane domin mu tattance su amma sun ki fitowa. Har yanzu mutum 20 kacal muka tattance kuma muna da mutum dari takwas da suka yi rijista a mazabar da nake aiki.

11:16 Gaskiya jama'a basu fito zabe sosai ba a garin kano. Daga Sadiq L. Umar

11:15 Shamaki Ubale Gashuwa jahar Yobe: Mu dai mun fito zabe kuma zamu kasa mu tsare mu raka mu jira domin a tabbatar mana da gwamna da 'yan Majalisun da muka zaba.

11:10 Mu talakawa muyi hakuri mufito zabe, Allah yazaba mana mafi alkhairi. Daga Shamsu Abdulhamid a Kano.

10:59 Ba kamar zabubbukan da suka wuce ba na yan majallisu da shugaban kasa inda mutane ke yin dogon layi a rumfunan zabe, yau ba haka abin yake ba a karamar hukumar Jibia dama wasu rumfuna a cikin garin katsina, inda zaka ga jami'an zabe ne ke jiran mutane su zo. Komi ya kawo hakan? Muh'd Sayyadi Filin-Sale, Jibia, Katsina.

10:55 Sagir Adamu Malumfashi BBC Hausa Facebook: Gaskiya abinda ya hana mutane fito kada kuri'a shine tsoran abubuwan da suka faru a baya.

10:52 Jama'a ba su fito kamar yadda ya kamata ba a cikin garin Gombe, saboda a cewarsu ba su gamsu da yadda zabukan baya suka gudana ba, kamar yadda Muhammad Ahmad ya shaida wa BBC ta wayar tarho.

10:50 Kudi dai kam ana rabawa jama'a tare da cewa abaka form kacika za a baka kujerar makkah da buhun taki in kazabesu kuma sai ka daga angani abin da kazaba, ance min haka ni sheda ne, ta faru garan. Daga Hafizu Balarabe Gusau jihar Zamfara.

10:48 Yanzu haka kusan ko ina an gama tantancewa a kwaryar birnin jahar Kano, amma gaskiya kona katin zabe yayi tasiri saboda ba'a futo sosai ba kamar satinda ya gabata. Abubakar Dan Yobe Daga Jahar Kano Najeriya.

10:45 A gaskiya mutane basu fito zabe ba a mazabar gandun albasa dake karamar hukumar birni dake kano amma ina rokon jama'a da suyi hakuri su fito zabe. Daga Kabiru Yusuf.

10: 44 Nura Abdulkarim NYSC (Daga Nassarawa Jihar Kano ): Muna gudanar da tantance masu kada kuri'a cikin lumana da kwanciyan hakali kuma jami'an tsaro suna kokari sosai wajan tabbatar da tsaro.

10:42 Har yanzu ana amfani da kudi wurin sayen kuru'un talakawa domin ni ganau ne. Daga Sagir Adamu Malumfashi jihar Katsina.

10:37 Jama'a ba su fito ba a Kontagora, Jihar Neja, kamar yadda Murtala Abasu ya shaidawa BBC ta waya.

10:33 Ina kira ga alummar kasata kada mugaza wajan yawaita dua'i, aski in yazo gaban goshi yafi zafi, allah kabamu shugaba na kwarai. Daga Hafizu Balarabe Gusau a jihar Zamfara.

10:31 Mahmud Adam BBC Hausa Facebook: Mu dai a jihar Gombe mutane basu fito sosai ba don zaben gwamna ba a jihar.

10:29 Naziru Daura BBC Hausa Facebook: Da'alama talakawa mun amsa kira yadda yakamata, domin idan ka zagaya kowace rumfa a garin Daura jama'a ne suka fito kwansu da kwar kata suna so su kada kuri'a. Allah ya bamu nasara.

10:26 Saleh Muhd Tahir BBC Hausa Facebook: Mu dai anan garin Kirenowa mutane ba su fito sosai ba domin duk rumfunan zabe guda shida na cikin gari ba jama'a sosai ma aikatan zabe ne ke zaune suna jiran mutane.

10:21 Wakilin BBC Yusuf Ibrahim Yakasai: Mutanen da suka fito a Kano ma ba su da yawa; su ma sun ce sun dawo daga rakiyar zabe saboda ba su gani a kasa ba.

10.20 A Lafia, Jihar Nasarawa, yawan mutanen da suka fito dai bai kai wadanda suka fito lokacin zaben shugaban kasa ba, saboda a cewarsu sun dawo daga rakiyar zabe tunda ba a ba su abin da suka zaba ba.

10:19 Garba Jibrin BBC Hausa Facebook: Mu dai anan karamar hukumar Mallam Madori jihar Jigawa jama'a basu fito ba sosai.

10:18 Talakawa muyi hakuri da zafin rana da ishin ruwa mu fito zaben wannan da zai kawo mana ci gaba a rayuwar mu. Atiku Abubakar, Kano.

10:17 Don Allah talakawa kar ku ji tsoron duk wata barazanar da jami'an tsaro zasu yi maku ku fito ku kada kuri'arku yau ranar 'yanci ce. Adamu Malumfashi.

10:16 Talakawa mu yi amfani da wannan dama ta yau don huce takaicin abinda yafaru abaya. Nazir One Daura.

10:15 A Gombe, jama'a ba su fito yadda ya kamata ba; mutane na korafin ba a ba su abin da suka zaba a wancan karon ba. A jihohin biyu dai an tsaurara matakan tsaro.

10:14 A Jihar Filato, jama'ar da suka fito ba yabo ba fallasa; amma ba su kai kamar lokacin zaben shugaban kasa ba.

10:13 A Lagos da sauran sassan yankin kudu maso yamma, mutane sun fito daidai gwargwado; ko da ya ke ba za a iya gaggawar yanke hukunci ba, sai lokacin fara kada kuri'a za a tabbatar. Sai dai a johohin Ekiti, da Osun da Ondo ba zaben gwamna sai na 'yan majalisun jihohi.

10:12 Yau ma na fito zan kada kuri'a ta fata na Allah yasa ranar dana sha makon daya gabata, yau ba zan shata ba, daga Aisha Matar Muhd Ahmad Idris a Kabuga Kano.

10:10 Yanzu haka ina gaban malamin zaben da suke tantance mutane a mazabar unguwar mu, amma gaskiya mutanen basu fito da yawa ba sakamakon kin yarda da sakamakon zaben shugaban kasa. Sako daga Babangida chairman kakabori Hadejia jahar Jigawa.

10:09 Yanzu haka na fito mazabata, abin mamaki mutane basu fito yin zabe so sai ba amma ina jin yana da alaka da damuwar yan Arewa akan sakamakon zaben shugaban kasa AMINU ABDU BAKA NOMA SANI MAI NAGGE KANO

10:08 A Jihar Rivers mutane da dama sun fito.

10:06 A Katsina, ko da yake da sauran lokaci, alamu na nuna cewa mutane ba su fito ba.

10:05 Ibrahim Malam BBC Hausa Facebook: Mutane dari tara ne suka yi rejista a mazabarmu ammai mutane {30} kawai suka fito zabe kawo yanzu, Allah ya kyauta ya zaba mana abinda yafi alkhari. Amin

10:03 A Maiduguri, mutane sun fito sosai a unguwar doki, duk da cewa bom ya tashi a unguwar lokacin zaben shugaban kasa. Mutanen sun ce tashin bom din bai sanyaya masu gwiwa ba; ko yau da safe ma bama-bamai sun tashi a garin na Maiduguri.

10:02 Kabiru Sakaina BBC Hausa Facebook: Babbar matsala a zaben yau itace rashin fitowar jama'a. Gaskiya yakamata al'ummah su fito.

10:01 Sakkwato ba zaben gwamna sai na 'yan majalisar jihohi. A wata rumfar zabe, awa daya bayan budewa mutane biyar kawai aka tantance.

09:59 Wakilin BBC Haruna Shehu Tangaza: A Jihar Kebbi mutane ba su fito ba, saboda korafin ko sun yi zabe ba za a ba su abin da suka zaba ba.

09.51 Matasan Nigeria ku yiwa Allah ku fito zabe kada kuyi fushi. Daga Musa Sikido Kwatalo hadejia jahar Jigawa.

09:50 Ibrahim Sarkiin Fulanin Facebook: Tuni an tantanceni ni da iyalaina a mazabata ta galadanchi.

09:49 Jazuli Baba Sadi daga Jalingo BBC Hausa Facebook: An tantance ni da zuwa na rumfar zabe, amma gaskiya jama'a basu fito sosai ba.