Amurka na kwashe 'yan kasarta daga Syria

Shugaban Amurka, Obama dana Syria, Asad
Image caption Amurka ta ce zama a Syria nada hatsari

Gwamnatin Amurka ta bayar da umarnin kwashe wasu ma'aikatan ofishin jakandancinta da ke kasar Sham, wato Syria.

Amurkan ta ce za ta kwashe 'yan kasarta daga Syrian ne saboda abin da ta kira, rudani da rashin tabbas a kasar.

Ma'aikatar hulda da kasashen wajen Amurkan ta ce, za a kwashe ma'aikatan ofishin jakadancin Amurkan da ofishin zai iya cigaba da gudana ba tare da su ba.

Tun farko dai Amurka ta ce, tana duba yiwuwar sanyawa Syria takunkumi saboda amfani da karfin da ya wuce kima da gwamnatin kasar ke yi akan al'ummar kasar.