Shugabannin Faransa da Italiya za su gana

Bakin haure akan hanyarsu ta zuwa Italiya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugabannin Faransa da Italiya za su tattauna

Shugabannin kasashen Faransa da Italiya za su yi wani taro a yau domin tantance matakin da za su dauka dangane da bakin haure da suka tsallaka cikin kasashensu.

Shugaban Faransa, Nikolas Sarkozy zai yi tattaki zuwa birnin Rome domin tattauna wannan batu tare da shugaban Italia, Silvio Berlusconi.

Silvio Berlusconi da kuma Nikolas Sarkozy za su tattauna akan yarjejeniyar nan da ta ba da damar zirga-zirga tsakanin kasashen Turai ba tare da wani shamaki ba.

Dubban bakin haure ne daga kasashen Larabawa suka shiga kasashen biyu a yunkurin kaucewa boren da ake yi a kasashensu.