Matsaloli sun dabaibaye zabuka a Najeriya

Matsaloli sun dabaibaye zabuka a Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Duk da matakan tsaron da aka dauka an samu sace-sacen kuri'u

Sace-sacen kuri'u da sauran alamun magudi sun mamaye zaben gwamnoni da 'yan majalisun jihohin da aka gudanar a wadansu jihohin Najeriya.

Mahukunta sun bayyana afkuwar irin wadannan abubuwa a jihohin Kano da Katsina a arewacin kasar, yayin da ya kuma afku a wadansu jihohin kudu da dama ciki har da Akwa Ibom da Delta da Rivers.

Akalla mutane goma sha uku aka kama sakamakon yunkurin sace akwatuna da sauran kayayyakin zabe a Jihar Bayelsa mai arzikin mai, kuma mahaifar Shugaba Goodluck Jonathan.

A cewar wani jami'in Hukumar Zabe, Abdullahi Umar Danyaya, sun samu labarin afkuwar irin wadannan matsaloli a jihar Kano.

"Mun shaida wa jami'an tsaro, kuma sun kaddamar da bincike domin gano musabbabin labarin da kuma daukar matakin da ya dace," kamar yadda ya bayyana.

'suka yi awon gaba da kayayyakin zabe'

A wajen garin Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom, wani dan jam'iyyar PDP da bai so a ambaci sunansa ba ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa wani mutum ya zo rumfar kada kuri'a "tare da wadansu yara biyar inda suka yi awon gaba da kayayyakin zabe".

"Daga nan sun wuce zuwa wata mazabar inda suka tayar da hankali, amma matasa sun yi kokari wajen kare kayan zaben".

Ya kara da cewa mutanen 'yan jam'iyyarsa ne, amma kuma bai amince da abin da suke aikatawa ba.

Najeriya ta yi kaurin suna wajen sace-sacen akwati a lokutan zabe, amma ta dauki matakan kawo karshen al'amarin a zabuka ukun da aka shirya a wannan watan.

Masu sa ido dai sun nuna gamsuwa da zabuka biyun da aka gudanar a baya--na 'yan majalisun tarayya da kuma shugaban kasa.

A ranar Talata, Shugaba Jonathan ya bayyana cewa "lokacin da ake satar kuri'u ya wuce a tarihin kasar."

Zaben gwamnonin na zuwa ne bayan da jama'a da dama suka rasa rayukansu sakamakon hargitsin da ya biyo bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar.