Bam ya tashi a Pakistan

Taswirar Pakistan Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Bam ya tashi a Pakistan

Bam ya tashi a birnin Karachi da ke Pakistan a wani hari da aka kaiwa wasu motoci kirar bos da ke dauke da jami'an gwamnatin kasar.

Bam din ya hallaka akalla mutane biyu, yayin da wasu mutanen sha biyar suka jikkata.

Daya bos din dai na dauke ne da jami'an sojan ruwa na Pakistan din, yayin da dayar kuma ke dauke da wasu jami'an tsaro.

'Yan sandan birnin na Karachi dai sun ce, basu tabbatar ba ko harin na kunar bakin wake ne.