Nigeria: ana jiran sakamakon zaben gwamnoni

Zabe a Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ko za a iya zabe marar magudi nan kusa a Najeriya kuwa?

A Nijeriya, yanzu haka dai ana ci gaba da kirga kuri'u bayan zaben Gwamnoni da 'yan majalisun jihohi da ma na tarayya a wasu wuraren, da ba a yi ba a baya ba.

Rahotanni dai na nuna cewa a jihohi da dama ba a samu fitowar jama'a sosai ba, musamman ma a arewacin Nijeriya.

Jihohi 24 cikin 36 ne dai aka yi zaben gwamnoni da 'yan majalisun dokoki.

Ba a yi zabe a jihohi biyar ba saboda wani umurnin kotu da ya hana yin zaben, saboda gwamnonin jihohin ba su cika wa'adin shekaru hudu da tsarin mulki ya tanadar ba.

Haka nan kuma kamar yadda aka sani hukumar zabe ta dage zaben a jihohin Kaduna da Bauchi zuwa jibi, sakamakon tashin hankalin da ya barke, bayan zaben Shugaban kasa na makon jiya.

Sai an ba da rahoton satar akwati, da dangwalen kuri'u don magudi, inda har kwamishin zabe ya kama ana yi ma PDP dangwalen kuri'u ba a wata sakatariyar gwamnati a jihar Katsinia.