Yau ake zaben gwamnoni a Najeriya

Wata mata a lokacin da ta ke kada kuri'a a zaben Najeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yau ake gudanar da zaben gwamnoni a Najeriya

'Yan Najeriya za su kada kuri'a a zaben da za'a fara nan gaba a yau, kuma wannan shi ne zabe na uku a jerin zabukan da ake yi a kasar.

Rahotanni na cewa tuni mutane suka fara fita rumfunan zaben.

An dai tsaurara matakan tsaro domin zaben na gwamnonin jihohi da kuma 'yan majalisun dokoki na jihohi.

Akwai dai zaman zullumi a sassa daban-daban na Najeriyar, yayin da aka kafa shingen bincike akan manyan titunan kasar.

Koda a safiyar yau, sai da aka ji karar fashewar wani abu da ake zaton bam ne a birnin Maiduguri na jihar Barno.

Daruruwan mutane ne suka mutu a tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa a makon jiya.