Mutane shidda sun mutu sakamakon wani harbi a Kabul

Kungiyar tsaro ta NATO a Afghanistan ta ce an kashe ma'aikatanta yan kasashen waje su takwas da kuma wani dan kasuwa a lokacin da wani matukin jirgin saman soji na kasar Afghanistan ya bude musu wuta, bayan wata sa -in -sa tsakaninsu a filin saukar jiragen sama dake birnin Kabul.

Sai dai an harbe mutumin har lahira a lokacin da suka yi musayar wuta.

Wanan dai shi ne lamarin na bayan baya a jerin munanan abubuwan da suka auku a cikin sansanin soji ko kuma ginin gwamnati, wuraren da kungiyar taliban suka fi kaiwa hari.

Wakilin BBC ya ce ba a fitar da sunayen kasashen sojojin da suka mutu ba ,sai an sanar da iyalansu.Jamian Afghanistan sun kuma tabatar da mutuwar matukin jirgin saman a lokacin da suka yi musayar wuta .