Zaben gwamnoni: PDP na taka rawar gani

zaben gwamnoni a Najriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An samu rahotannin sace-sacen kuri'u a sassa da dama na kasar

Sakamakon zaben gwamnoni da 'yan majalisun jihohi da aka gudanar jiya a Najeriya, ya nuna cewa jam'iyyar PDP mai mulkin kasar na samun gagarumar nasara a jihohi da dama na kasar.

Sakamakon da aka bayyana a jihar Enugu ya nuna cewa gwamnan jihar Sullivan Iheanacho Chime na jam'iyyar PDP ne ya lashe zaben, da kuri'u dubu dari hudu da goma sha tara, da dari bakwai da casa'in.

Yayin da Cif Okey Ezea na jam'iyyar Labour ya zo na biyu da kuri'u dubu talatin, da dari daya da talatin da biyar.

Haka ma gwamnonin jam'iyyar PDP ne suka sami nasara a jihohin Abiya da Ebonyi.

A jihar Jigawa ma, gwamna Sule Lamido na jam'iyyar PDP ne ya sake lashe zaben, da kuri'u sama da dubu dari uku, inda ya kayar da Alhaji Badaru na jam'iyyar ACN.

Haka kuma jam'iyyar PDPn ta lashe kujerun majalisar Dokoki 29 daga cikin 30 da ake da su a jihar.

A jihar Kano ma...

A jihar Kano ma, sakamakon da Hukumar zabe ta bayyana ya nuna cewa dan takarar jam'iyyar PDP Dr Rabi'u Kwankwaso ne ya lashe zaben inda ya zarta dan takarar jam’iyyar ANPP mai mulkin jahar da sama da kuri’u dubu 60.

Sai dai jam’iyyun ANPP da na CPC sun yi watsi da sakamakon, bisa zargin tafka magudi.

A jihar Sokoto ma, jam'iyyar PDP ce ta lashe baki dayan kujerun 'yan majalisar jihohi 30 da aka kada kuri'a a kansu.

Can ma a jihar Kebbi, jam'iyyar PDP ce ta yi nasara inda gwamna mai ci Alhaji Saidu Dakingari ya lashe zaben.

A jihar Niger kuwa, sakamakon da aka bayyana kawo yanzu ya nuna cewa jam'iyyar PDP ce kan gaba a sakamakon kananan hukumomi 23 daga cikin 25 na fadin jihar.

A jihar Gombe ma, dan takarar jam'iyyar PDPn ne, Alhaji Ibrahim Dan kombo ya lashe zaben yayinda a jihar Pilato sakamakon da aka bayyana kawo yanzu ya nuna cewa PDPn ce ke kan kan gaba a zaben gwamna da na 'yan majalisun jihar.

A Jihar Borno, sakamakon da Hukumar zabe ta bayyana ya nuna cewa Alhaji Kashim Shattima na jam'iyyar ANPP ne ya lashe zaben.

A jihar Yobe ma jam'iyyar ANPP din ce ta yi nasara inda gwamna mai ci, Alhaji Ibrahim Gaidam ya lashe zaben.

'Ya adawa ma sun taka rawar gani

Sai dai a yankin Kudu maso Yamma, jam'iyyar ACN ce ta lashe zaben gwamna da na 'yan majalisun dokoki a jihar Legas.

ACN din ce kuma ta lashe zaben kujerun majalisar dokokin jihar Osun.

Haka ma a jihar Oyo hukumar zabe ta bayyana Mr. Abiola Ajimobi , dan takarar jam'iyar ta ACN a matsayin awnda ya lashe zaben inda ya doke gwamnan jihar na jam'iyyar PDP Cif Alao Akala da kuma na Accord Party tsohon gwamnan jihar Rasheed ladoja.

Sakamakon zaben jihar Nasarawa, ya nuna cewa jam'iyyar CPC ce ta lashe zaben gwamnan jihar, inda Tanko Al-makura ya kada gwamna mai ci a yanzu Aliyu Akwe Doma na jam'iyyar PDP.

Hakazalika jam'iyyar CPCn ta lashe kujeru da dama na 'yan majalisar jihohi a jihar ta Nasarawa.

An dai gudanar da zabukan ne cikin rudani da zargin satar kuri'u a sassa da dama na kasar, inda masu sa'ido suka nuna damuwa kan cewa kasar ta kama hanyar komawa gidan jiya.