Bangarorin Falesdinawa sun cimma 'yarjejeniya

Shugaban Falesdinawa, Mahmoud Abbas Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban Falesdinawa, Mahmoud Abbas

Kungiyoyin Falasdinu masu adawa da juna wato Fatah da Hamas sun cimma 'yarjejeniya wadda za ta share fagen samun gwamatin hadin kan kasa da kuma yin zabe a kasar.

Bangarorin biyu sun gana da juna a tattaunawar da gwamnatin Masar ta shirya.

Wakilin BBC ya ce ba'a fitar da cikaken bayanai akan yarjejeniyar da aka cimma ba amma jamian kungiyar Hamas a birnin alqahira sun ce sun cimma matsaya da abokane hamayyasu wato kungiyar Fatah akan yadda za'a kafa gwamnatin rikon kwarya.

Sai dai Firayim ministan Israila Benjamin Netanyahu ya maida martani inda ya yi gargadin cewa ya zama dole ga hukumomin Falasdinu su zabi zaman lafiya da Israila ko Hamas.