Ana jiran sakamakon zabe a Najeriya

Wani mai kada kuri'a a zaben Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ana jiran sakamakon zabe a Najeriya

A Najeriya ana cigaba da kidaya kuri'un da jama'ar kasar mafi yawan jama'a a Afirka suka kada a kashi na uku na zabukan da kasar ta shirya.

Jiya Talata ne dai 'yan Najeriyar suka gudanar da zaben gwamnonin jihohinsu.

Su dai gwamnoni a Najeriya suna da karfin gaske saboda sune ke rike da akalar dimbin dukiyar da ake kasaftawa jihohi daga baitul malin tarayya.

Kuma irin dukiyar jama'a da gwamnonin ke rike da ragamarta wani kan kai yawan kasafin kudin shekara na wasu kananan kasashen yammacin Afirka.

Sai dai kuma mutane ba su fito ba sosai a zaben na jiya.