An kashe masu zanga-zanga akalla biyar a Yemen

Masu zanga-zanga a Yemen Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masu zanga-zanga a Yemen

Rahotani daga Yemen sun ce masu zanga- zangar kin jinin gwamnati akalla biyar ne suka hallaka yayinda da dama su ka samu raunuka a Sana'a babban birinin kasar.

Rahotanin sun ce dakarun kasar da kuma yansanda dake sanye da farin kaya sun budewa masu zanga zangar wuta.

Wasu Hotuna talibijin da aka samu daga wurin kamfanin dilanci labaru na reuters sun nuna lokacin da matasa ke gudu da ihu da kuma wuta na tashi.

Hakazalika an kashe wani dan adawa a kudancin birnin Aden.