Amurka ta bayyana Hamas a matsayin kungiyar ta'adda

Shugaban Amurka Barack Obama
Image caption Fadar gwamnatin Amurka ta White House ta bayyana cewar dole ne duk wata gwamnatin Palasdinawa ta amince da Isra'ila a matsayin kasa.

Isra'ila da Amurka sun maida martani cikin sanyin gwiwa game da sanarwar da kungiyoyin Fatah da Hamas suka bayar, inda suka amince da wani shiri na sasantawa.

Fira Ministan Isra'ilan Benjamin Netanyahu, ya shaidawa hukumomin Palasdinu da kungiyar Fatah ke jagoranci cewa, Isra'ila ba za ta taba samun zaman lafiya ba, muddin su na hade da Hamas.

Kakakin Fira Ministan Isra'ilar Mark Regev yace, magana ta gaskiya ita ce, zaman lafiya ba zai yiwu ba, ganin irin yadda al'amarin yake. Yace manufa, Hamas ta fito fili ta bayyana haka. Hamas ba ta son duk wata sasantawa.

A bangare guda kuma fadar gwamnatin Amurka ta White House ta fidda sanarwar dake cewa Hamas kungiyar 'yan taadda ce, don haka dole duk wata gwamnatin Palasdinawa ta amince da Isra'ila a matsayin kasa.