Yau ake zaben gwamnoni a jihohin Kaduna da Bauchi

Zabe a Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption A yau ake gudanar da zaben gwamnonin jihohin Kaduna da Bauchi a arewacin Najeriya bayan da aka dage zabukan daga ranar 26 ga watan da aka ciki.

A Najeriya, a yau ne ake gudanar da zaben gwamnoni a jihohin Bauchi da Kaduna bayan dage zaben daga ranar 26 ga wannan watan sanadiyyar rikice rikicen da suka biyo bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar makonni biyu da suka gabata.

A jahar Kaduna dai inda wannan rikici ya fi kamari, za a gudanar da zaben ne karkashin tsauraran matakan tsaro, yayin da wasu, musamman 'yan jam'iyyun adawa ke cewa ya kamata a sake dage ranar gudanar da shi domin samun cikakken kwanciyar hankali.

To sai dai hukumar zaben ta ce ba gudu ba ja da baya

A can jahar Bauchi ma an tsaurara matakan tsaro a jahar musamman ma garin Bauchi domin shirin zaben.

Sai dai 'yan adawa sun koka ga dokar hana zirga zirgar dake aiki a fadin jihar, suna masu zargin cewar maiyiwuwa jam'iyyar PDP mai mulki tayi amfani da wannan dama wajen tafka magudi

To sai dai jami'an gwamnatin Bauchin sunce babu wani abun fargaba, kuma sun tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin jama'a

Baya ga gwamnan jahar ta Bauchi Malam Isa Yuguda na jam'iyyar PDP, sauran 'yan takarar da zasu fafata wajen neman kujerar gwamnan jahar sun hada da Sanata Baba Tela na jam'iyyar adawa ta ACN. Hakazalika akwai kuma Sanata Sulaiman Nazifi na jamiyar adawa ta ANPP. Sai kuma jam'iyyar CPC wacce 'yan takara hudu kowannensu ke ikirarin cewar shine dan takara wadanda suka hada da Hon. Yusuf Maitama Tugga da Injiniya Nuhu Gidado da kuma sabid Mahmud

Sai dai hukumar zaben Najeriya wato INEC daga baya ta bayyana sunan Hon Yusuf Maitama Tugga da cewar shine dan takarar jam'iyyar ta CPC