Zaben gwamna a Kaduna da Bauchi

A Nijeriya, yanzu haka ana can an fara kirga kuri'un zaben gwamna da aka kammala a jihohin Kaduna da Bauchi.

An dage zaben a jihohin zuwa yau ne, a sakamakon tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa, a wasu yankuna na arewacin Nijeriya.

Rahotanin dake fitowa daga Kaduna na nuna cewar ba a samu fitowar jama'a sosai ba, lamarin da wasu ke dangantawa da yawan jami'an tsaro da aka baza, yayinda wasu ke cewa sun ki fitowar ne, saboda ko sun yi zaben, ko ba su yi ba, magudi za a tafka.

Can kuma a jahar Bauchi a wannan karon ba batun nan na a kasa a tsare sabo da dokar hana fitar dare, wadda aka mayar daga karfe takwas na yamma zuwa karfe shida na safe.

Masu kada kuri'a a jahar ta Bauci dai sun ce an samu matsaloli da dama ciki harda satar akwatunan zabe da barazana ga ma'aikatan zabe, musamman a kananan hukumomi dake nesa da Bauchi babban birnin jihar.