Ruwan sama ya hallaka daruruwan mutane a Amirka

Barnar ruwan sama da iska a Amirka Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Barnar ruwan sama da iska a Amirka

A Amirka mutane fiye da 250 ne aka tabbatar sun hallaka kawo yanzu, sakamakon ruwan sama da iska mai karfin gaske, a yankin kudancin kasar.

An kafa dokar ta baci a jahar Alabama, wadda mahaukaciyar guguwar mai tafe da ruwa ta fi yiwa illa.

Shugaban kasar, Barack Obama, ya nuna alhininsa game da asarar rayukan da aka samu.

Ya ce gwamnatinsa za ta yi iyakacin kokarinta, domin agazawa mutanen da lamarin ya shafa.

Gobe Juma'a shugaban Amirkan zai ziyarci jahar Alabama, domin ganin barnar da mahaukaciyar guguwar mai dauke da ruwa ta haddasa.