NATO ta zargi dakarun Gaddafi da dasa nakiyoyi

Birnin Misrata Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Birnin Misrata

Kungiyar tsaron NATO ta zargi dakaru masu biyaya ga jagoran Libiya, Kanar Gaddafi, da dasa nakiyoyi a gabar tekun birnin Misrata da ke hannun 'yan tawaye, wanda kuma aka yiwa kawanya.

Wani babban jami'in NATOn ya ce, jiragen ruwan kungiyar na yaki, sun kama kwale-kwale masu yawa, kusa da tashar ruwan Misrata.

Ya ce, yin amfani da nakiyoyin ya nuna cewa, gwamnatin Libiyar ba ta mutunta dokokin kasashen duniya ko kadan.

Dakarun gwamnatin Libiyar sun killace birnin Misratar, wanda ya dogara da tashar ruwan wajen samun kayayakin agaji da makamai.

Daga tashar ce kuma ake kwashe 'yan gudun hijira da wadanda suka jikkata.