Dakarun Syria sun yi harbi kan masu zanga zanga

Dubun dubatar masu adawa da gwamnatin Syria sun gudanar da wani gangami a garuruwa da birane daban daban dake fadin kasar duk da cewa an tsaurara matakan tsaro.

A damascus babban birinin kasar rahotanni sun ce an harba hayakin mesa hawaye domin tawartsa jama'a dake kokarin gudanar da zanga zanga .

A birinin Dar'aa sun ce sojoji sun yi ta harbe harbe domin hana jama'a halatar salah juma'a ko kasancewa a cikin masu zanga zangar.

Wakilin BBC ya ce daga garin Kurdawa na Qameshli dake Arewa zuwa ga garuruwa da kuma kauyukan dake can kudanci bayanai sun ce an gudanar da zanga zanga bayan salar juma'a a garuruwa da dama da kuma birane dake fadin kasar