Kungiyar NATO da 'yan adawa sun yi watsi da tayin Gaddafi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yan tawaye a birnin Misrata

Kungiyar tsaro ta NATO da 'yan tawayen Libya sun yi watsi da tayin da shugaban Libya, Kanar Gaddafi ya yi masu na kawo karshen fada a kasar da kuma fara tattaunawa.

Wani kakakin kungiyar ta NATO, Chris Riley ya ce akwai sharrudan da ya kamata Kanar Gaddafi ya cika, idan yana son tattaunawa.

Ya ce zasu cigaba da kai hare-hare har sai sojojin gwamnatin Libyar sun daina kai hari da kuma yin barazana a kan fararen hula.

Sannan kuma gwamnatin kasar ta tabbatar cewa ta kyale an kai kayan agaji ga wadanda suke bukata.

A wata sanarwa da suka bayar a Hedwatarsu dake birnin Benghazi, shugabannin 'yan tawayen sun ce tayin na Kanar Gaddafi, ba shi da wani sahihanci, suna masu cewa wata dabara ce da dama ya sha amfani da ita.

A wani jawabi ta gidan talabijin, Kanar Gaddafin dai ya ce a shirye yake ya tattauna da Faransa da Birtaniya da kuma Amirka, idan suka dakatar da hare-haren da suke kai ma kasarsa.