Mutum 16 ne suka rasu sakamakon fashewar bam a Morocco

Ginin da bam ya yi wa kacha-kacha a Morocco Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Harin bam din da aka kai a kasar morocco ranar alhamis na nuni da cewar baki 'yan kasashen waje ake hara

Adadin mutanen da suka rasu sakamakon fashewar bam a birnin Marrakesh na kasar Morocco sun karu zuwa mutum goma sha shidda.

Akwai dan shekaru goma da haihuwa cikin wadanda suka rasun, wanda ga alamu 'yan kasashen waje aka hara.

An gano gawarwakin dan birtaniya guda, da 'yan kasar Canada guda biyu, da Faransawa 7 da kuma dan kasar Holland guda.

Ministan sadarwar Moroccon Khalid Naciri, ya ce lokaci yayi da al'ummar Moroccon ke da hurumin sanin irin sauye sauyen da kasar ke yi a daidai lokacin wannan hari na 'yan Al-Qaeda.

Ya ce wadanda suka kai hari kan Morocco na kokarin muzgunawa kasar ne, da yiwa fannin bude idanunta cikas da kuma yin illa ga matsayinta a yankin Mediterranean.