Ana cigaba da korafi a Najeriya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Zaben Najeriya

'Yan adawa a Najeriya na ta korafin cewa an yi ma su magudi a zabukan kasar da aka gudanar yayin da jam'iyyu masu mulki ke musanta hakan.

A jihar Gombe 'yan adawa sun ce kwace aka yi a jihar ta Gombe ba zabe ba.

Alhaji Abubakar Aliyu wanda shi ne dantakarar gwamna na jam'iyyar CPC wanda ya zo na biyu a zaben ya shaidawa BBC cewa an kasa amfani da na'urar kwamfuta kamar yadda alkwaranta a wajen zaben.

A cewarsa wanan abu dubuwa ne.

To sai dai kuma kakakin jam'iyyar PDP mai muki a jihar, Adamu Abdu Gadam, ya musanta zargin magudin.

A jihar Bauchi ma dai ana ci gaba da cece-kuce kan sakamakon zabukan da aka kamala jiya inda 'yanadawa ke zargin jam'iyyar PDP me mulki da tafka magudi, ita kuma tana musantawa.

Haka lamarin yake a jihar Filato inda a karon farko a tarihin demokradiyyar kasar gwamna da mataimakiyarsa suka kalubalanci juna a zaben karkashin inuwar jam'iyyu mabambanta.

Hukumar zabe a kasar ta ce duk wanda bai gamsu da zaben ba yana iya garzayawa kotu domin gabatar da kukansa.