Sojojin Syria sun karbe iko a masalacin dake Dera'a

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu zanga zanga a Syria

Mazauna birnin dar'aa a Syria sun ce sojoji sun karbe iko a masalacin da ya rika jan hankalin masu zanga zangar kin jinin gwamnati .

Shaidu a tsohon birnin Dera'a sun ce dakaru da suka samu goyon banyan tankokin yaki sun kai ma masalacin Omari farmaki.

Bayanai sun ce rundunar sojin kasar ta girka marhaba a saman masalacin.

Da dama daga cikin mutane sitin da aka kisyasta sun hallaka a lokacin zanga zangar da aka gudanar a sasa daban daban dake fadin kasar ranar juma'a an harbe su ne a ciki ko kusa da birnin Dera'a.