Jami'an CIA za su yi bincike a Pakistan

Jami'an tsaro na gadin gidan Osama a Abbottabad Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jami'an tsaro na gadin gidan Osama a Abbottabad

Kafofin yada labarai na Amurka sun bayar da rahoton cewa Pakistan za ta kyale Hukumar Leken Asiri ta Amurka, CIA, ta yi bincike a gidan Osama bin Laden a Abbottabad.

Za a kyale hukumar ta CIA ne ta aike da wadansu kwararru don su gudanar da bincike a gidan na Osama bin Laden, su kuma tattaro bayanan da zaratan sojojin na Amurka ba su samu damar kwasa ba.

Jaridar Washington Post ta ce a makon da ya gabata mataimakin shugaban hukumar ta CIA, Michael J. Morell, ya gana da shugaban Hukumar Leken Asiri ta Pakistan, ISI, a Islamabad, inda suka amince a baiwa CIA din wannan dama.

Rahotanni sun ce nan da 'yan kwanaki kadan jami'an na Amurka za su isa kasar ta Pakistan da na'urori na zamani don gano abubuwan da aka binne a karkashin kasa ko aka boye a cikin gini.

Wannan ba kawai dama ce ga Amurka ta yi binciken kwakwaf a kan kayayyakin Osama ba, wani muhimmin mataki ne na gyara dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, wadda ta yi tsami bayan kashe Osama bin Laden da kuma kama wani ma'aikacin tsaro na CIA wanda ya harbe 'yan Pakistan biyu har lahira.