Strauss-Kahn ya ajiye shugabancin IMF

Shugaban IMF, Dominique Strauss-Kahn Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban IMF, Dominique Strauss-Kahn

Shugaban Asusun ba da Lamuni na Duniya, IMF, Dominique Strauss-Kahn, ya yi murabus daga mukaminsa.

Murabus din na Mista Strauss-Kahn ya zo ne bayan matsin lamba a ciki da wajen kasar Faransa.

A yau Alhamis ne dai ake sa ran shugaban na IMF zai bayyana a gaban wata kotun birnin New York wadda za ta yanke hukunci a kan ko za a bayar da belinsa.

Ana tsare da Mista Strauss-Kahn ne a wani gidan yarin da ya yi kaurin suna a birnin New York; daga can ne kuma zai koma Kotun Hukunta Manyan Laifuffuka ta yankin Manhattan inda za a saurari bukatar sa ta a bayar da belin nasa.

Lauyoyin Mista Strauss-Kahn dai za su yi yunkurin gamsar da wani alkalin na daban cewa ya kamata a bayar da belin sa yayin da ya ke kokarin wanke kansa daga zargin da ake masa.

Lauyoyin za su kuma nemi a bayar da belin Mista Strauss-Kahn a kan sama da dala miliyan daya; sannan za su yi tayin ya rika sanya wata na'ura a kwauri wadda za ta bayar da damar sa ido a kansa, a kwace fasfonsa, kuma a yi masa daurin talala.

Ga alama dai ranar Litinin din da ta gabata alkali ya yarda da masu shigar da kara cewa Mista Strauss-Kahn ka iya tserewa saboda har ya shiga jirgi yana shirin barin kasar aka kama shi ranar Asabar.

Sai dai masana harkokin shari'a na ganin cewa mai yiwuwa wani alkalin na daban ya yanke shawara sabanin hakan.

Gobe Juma'a ne kuma kotun za ta yi wani zama na daban, lokacin da ake sa ran masu taimakawa alkali yanke hukunci su yanke shawara a kan ko za a tuhumi Mista Strauss-Kahn da laifin yunkuri aikata fyade ko a'a.

Matsin lamba a kan Dominique Strauss-Kahn dai ya yi ta karuwa a ciki da wajen kasar Faransa.

Sakataren baitulmalin Amurka, Timothy Geithner, shi ne ya fara yin kira gare shi ya ajiye aikinsa, sannan shugaban jam'iyyar UMP mai mulki a Faransa, Jean Francois Cope, wanda ya ce bai ga dalilin da zai sa Mista Strauss-Kahn ya ci gaba da rike mukamin ba.

Jam'iyyar adawa ta Socialist dai, wadda ta ke sa ran zai yi mata takarar shugabancin kasa badi, ta nuna goyon baya ga Mista Strauss-Kahn, amma akwai fargabar cewa idan ya dage sai ya ci gaba da rike mukamin zai iya bata sunan Faransa da ma jam'iyyar tasa.

Akasarin manazarta da ma tsofaffin jami'an baitulamalin Amurka na ganin cewa Washington za ta mara baya ga wani daga Turai don ya maye gurbin Mista Strauss-Kahn.

Da ma dai ko ba wannan tuhuma, a karshen shekarar nan ne Mista Strauss-Kahn ya yi niyyar ajiye aikin nasa.

Ana ganin ministar kudi ta Faransa, Christine Lagarde, za ta nemi mukamin, to amma shekaru ashirin da shida ke nan Faransar na rike da wannan mukami.

Shugabar Jamus ma, Angela Merkel, za ta so ta ga wani daga kasarta ya dare mukamin.

Karin bayani