Yau ake rantsar da Alassane Ouattara

Shugaba Alassane Ouattara na Ivory Coast Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Alassane Ouattara na Ivory Coast

Shugabannin kasashen duniya fiye da ashirin ne za su halarci bikin rantsar da shugaban kasar Ivory Coast, Alassane Ouattara a yau.

Za a gudanar da bikin ne da nufin kawo karshen kokawar mulki tsakanin Mista Ouattara da kuma Laurent Gbagbo, wanda ya ki amincewa da shan-kaye a zaben shugaban kasar da aka gudanar.

Mutane fiye da dubu uku ne dai suka hallaka a tashe-tashen hankulan da suka biyo bayan gudanar zaben shugaban kasar.

Shugaban kasar zai tashi tsaye wajen kawo karshen rikicin kabilancin da kungiyoyin kare hakkin dan-Adam suka zargi bangariorin biyu da rurutawa, da kuma aikata kisa, da fyade, da wadansu miyagun laifuffuka.