An yi musayar wuta daren jiya a Maiduguri

'Yan sanda a Maiduguri
Image caption 'Yan sanda na bincikar bom a Maiduguri

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno a arewacin Najeriya sun ce an shafe fiye da mintuna arba'ain a daren jiya ana musayar wuta.

An yi dauki-ba-dadin ne tsakanin jami'an tsaro da 'yan kungiyar nan ta Jama'atu Ahlis Sunna Lid Da'awati Wal Jihad, wadda aka fi sani da Boko Haram, a lokacin da ‘yan Boko Haram din suka kai hari a caji ofis na Ibrahim Taiwo da ke kan titin zuwa tashar Baga a tsakiyar birnin.

Wakiliyar BBC ta ce an fara jin harbe-harbe ne da misalin karfe takwas na dare, al’amarin da ya razan mazauna wadansu daga cikin unguwannin birnin.

Mazauna unguwannin Rukunin Gidaje na Tarayya, da Jajeri, da Bolori, da Pompomari sun bayyana cewa ruf da ciki suka yi su da iyalansu a dakunansu don gudun harsashin da ka yi batan kai.

Rundunar 'yan sandan jihar ta Borno dai ta tabbatar da aukuwar wannan al'amari, tana cewa da ma dai tana labarin cewa ‘yan kungiyar ta Boko Haram na shirin kai hari a kan caji ofis din, don haka ta kara jami’ai a wurin.

A cikin 'yan makwannin nan dai an samu yawaitar kai hari da kashe-kashe a birnin na Maiduguri.