Yau Shugaba Obama zai gana da Netanyahu

Benjamin Netanyahu Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Firayim Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu

Nan gaba a yau ne Shugaba Obama na Amurka zai gana da Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a Washington.

Ganawar dai za ta zo ne bayan Shugaba Obama ya gabatar da wani jawabi mai zafi wanda a ciki yake cewa ana bukatar zaman lafiya yanzu fiye da ko wanne lokaci a baya.

Mai yiwuwa wannan ganawa tsakanin shugabannin biyu wadanda suka samu sabani a baya ta yi tsauri.

Jawabin Mista Obama dai bulaliyar kan hanya ce: ya yi kallon hadirin kaji ga bukatar Falasdinawa ta wani kudurin Majalisar Dinkin Duniya wanda zai ayyana kasar Falasdinu, yayin da kuma ya dora ayar tambaya a kan yadda Isra'ila za ta shiga tattaunawa da kungiyar Hamas wadda ba ta yarda da wanzuwar Isra'ilan ba.

Sai dai kuma ya bayyana sauyi a manufofin Amurka, yana cewa ya kamata iyakokin Isra'ila da Falasdinu su ginu a kan tubalin da aka shata a shekarar 1967.

Wannan dai shi ne ginshikin tattaunawar zaman lafiya a shekaru fiye da goman da suka gabata, amma ba shugaban Amurkan da ya taba fitowa baro-baro ya fadi hakan.

Mista Netanyahu dai ya yi watsi da shawarar Obama cewa amincewa da kasashen Falasdinu da Isra'ila a bisa iyakokin na 1967 ne ginshikin samar da zamn lafiya.

Mista Netanyahu ya ce aiwatar da wannan tsarin zai mayar da dimbin al'ummun Yahudawa karkashin iyakokin kasar Falasdinu.

Karin bayani