Amurka ta kakabawa Shugaba Assad takunkumi

Shugaba Bashar Al Assad na Syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Bashar Al Assad na Syria

A karo na farko, kasar Amurka ta sanyawa shugaban kasar Syria Bashar Al Assad takunkumi, shi da wadansu manyan jami'an kasar su shida, saboda cin zarafin bil-Adama da ta ce sun aikata a lokacin zanga zangar nuna kyamar gwamnati.

Za a kwace duk wata kadara da suke da ita a kasar Amurkar.

Wani wakilin BBC a Washington ya ce yanzu Amurkan tayi imanin cewa Shugaba Bashar Al Assad ne ke da alhakin musgunawar da aka yiwa 'yan adawar kasar.

Wakilin namu ya kara da cewa Amurka na yiwa Shugaba Assad gargadi ne na karshe: ko ya jagoranci mika mulki ga zababbiyar gwamnati ko kuma ya tattara nasa-ya-nasa ya tafi.

Tun da farko dai Shugaba Assad ya amince da cewa dakarun tsaron kasarsa sun yi kuskure wajen shawo kan masu zanga zangar.

Wata 'yar jarida wadda aka tsare a kasar ta Syria a watan da ya gabata mai suna Dorothy Parvas, ta ce tasha dan karen duka dare da rana a lokacin da take hannu.

An tsare Miss Parvas, wacce take yiwa kafar yada labarai ta Al Jazeera aiki, har na tsawon kwanaki uku, bayan an zarge ta da yin cuwa-cuwar fasfo.

An dai tafi da ita zuwa kasar Iran, amma a yanzu an sake ta.

A lokacin da ake tsare da ita, ba a bata damar yin magana da kowa ba.

Dorothy ta kuma bayyanawa BBC irin halin da ta samu kanta a ciki a lokacin da ake tsare da ita a gidan kurkukun.

“Kana iya jin ana lakadawa mutane duka a wajen; kana iya jin kara da kuka.

“Za ka so ka tsohe kunnuwanka amma ya kamata wani ya saurari wadannan mutane, ya kuma fahimci halin da suke ciki”, in ji ’yar jaridar.

Karin bayani