Amurka ta yi kira ga Strauss-Kahn ya sauka

Dominique Strauss-Kahn Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dominique Strauss-Kahn

Sakataren kudi na Amurka, Timothy Geithner, ya ce Dominique Strauss-Kahn, wanda ke fuskantar tuhumar yunkurin aikata fyade, bai dace ya shugabanci Asusun ba da Lamuni na Duniya (IMF) ba.

Sakataren kudin na Amurka ya ce a bayyane ta ke cewa bai kamata Mista Strauss-Kahn ya ci gaba da tafiyar da al'amuran asusun na IMF ba, sannan ya yi kira ga asusun ya nada wani shugaba na wucin gadi.

Har yanzu dai asusun na IMF bai yi yunkurin tuntubar shugaban nasa ba, yayin da bayanai ke nuna cewa wadansu daga cikin mambobin hukumar daraktocin asusun sun nemi Mista Strauss-Kahn ya ajiye aiki nan take.

Tun ranar Asabar ne dai ake tsare da Mista Strauss-Kahn bayan kama shi da aka yi ana zargin sa da laifin yunkurin yi wa wata ma'akaciyar otal 'yar shekaru talatin da biyu da haihuwa fyade.

Bayan likitoci a gidan yarin sun auna shi, an sa Mista Strauss-Kahn a karkashin kulawa ta musamman inda masu gadi ke duba shi bayan ko wanne minti talatin don tabbatar da cewa bai yi yunkurin kashe kansa ba.

Sai ranar Juma'a ne dai shugaban asusun na IMF zai sake bayyana a kotu.

Wadda ke zargin Mista Strauss-Kahn din dai wata 'yar ci rani ce 'yar asalin kasar Guinea, da ke yammacin Afirka.