Najeriya za ta sauya manufofin diflomasiyya

Shugaba Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta yi sauye-sauye ga wadansu manufofinta na diflomasiyya, ta yadda za su dace da zamani.

Gwamnatin ta ce an shimfida ginshikin wasu manufofin ne tun lokacin da kasar ta samu mulkin kai a shekarar 1960, don haka akwai bukatar a yi musu kwaskwarima.

Dokta Aliyu Idi Hong, Minista a Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, ya shaidaw BBC cewa a wancan lokacin Afirka ce ginshikin manufar diflomasiyyar Najeriya; sannan kuma an karfafa cewa Najeriya ba za ta sa baki a harkokin wata kasa ba.

“Amma duniya ta yi tafiya”, in ji Dokta Hong, “mu ma mun samu ci gaba kwarai; kuma muna da [bukatu] da yawa, saboda haka aka ga ya kamata a sauya tsarin mu na diflomasiyya ta yadda zai dace da burin da muke son cimmawa”.

Dokta Hong ya kara da cewa za a yi amfani da diflomasiyyar Najeriya don ci gaban kasar da kuma samarwa mutanenta aikin yi.

Sai dai wadansu dattawa a kasar na ganin mutuncin Najeriya ya zube ta yadda duk wani kwaskwarima ba zai yi amfani ba.

A cewar Dan Masanin Kano, Alhaji Yusuf Maitama Sule, wanda tsohon minista ne a Jamhuriya ta Farko, kuma tsohon wakilin Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya, “Yanzu abin da ya ke gabanmu mu gyara gida—sai giji ta koshi a kan ba dawa—mu yi kokari a samu zaman lafiya, mu gyara siyasarmu, mu yi kokari mu gyara tattalin arzikin kasarmu, cin hanci da rashawa a yi kokari a yi yaki da su, a samu tsaro mai kyau a cikin kasa...”