Gwamnatin Uganda ta daura yaki da 'yan jarida

Shugaba Yoweri Museveni
Image caption Shugaban Uganda Yoweri Museveni

Kasa da mako guda bayan rantsar da shi a karo na hudu, Shugaba Yoweri Museveni na Uganda ya bayar da sanarwar daura damarar yaki da wadansu kafofin yada labarai na kasar da na waje.

Shugaba Museveni ya yi hakan ne a wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta Uganda ta fitar, wadda a ciki ya zargi kafofin yada labaran da ingiza magoya bayan shugaban 'yan adawar kasar, Kizza Besigye, wanda gwamnatin kasar ta Uganda ta zarga da laifin tayar da zaune tsaye.

Shugaban na Uganda ya kuma ce wadannan kafofin yada labarai, wadanda suka hada da Aljazeera da BBC da kuma wadansu kafofin yada labarai na cikin gida, makiya ci gaban kasar Uganda ne kuma ya kamata a yi huldar da ta dace da su.

Ko da yake Mista Museveni bai bayyana irin matakan da gwamnatin za ta dauka a kan wadannan kafofin yada labarai ba, irin kalaman da sanarwar tasa ta yi amfani da su ka iya nuna cewa gwamnatin ta sa kafar wando guda da 'yan jarida na gida da waje, wadanda ya ce ba sa ba da rahoto a kan miyagun ayyukan 'yan adawar.

Gwamnatin dai ta zargi 'yan adawar da yin jifa a kan jerin gwanon motocin da ke dauke da shugabannin wadansu kasashen Afirka biyu, ciki har da na Najeriya, wadanda suka je kasar don halartar bikin rantsar da Mista Museveni.

Dimbin magoya bayan shugaban 'yan adawa Kizza Besigye ne dai suka tarbe shi yayinda ya koma kasar a daidai lokacin da ake rantsar da shugaban kasar bayan ya yi jinya a Kenya.