Harin NATO ya yi sanadiyyar rasuwar dan Kanal Gaddafi

Wajen da harin NATO ya lalalata a gidan Saiful Arab Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mai magana da yawun gwamnatin Kanal Gaddafi ya bada sanarwar rasuwar Saiful Arab da wasu jikokin gidan Gaddafiin su uku, bayan harin sojin kawancen NATO

Mai magana da yawun shugaba Ghaddafi, Ibrahim Moussa ya bada sanarwar rasuwar Saiful Arab, karamin dan Kanal Gaddafi.

Rahotanni sunce shugaban Libyan Mu'aammar Gaddafi ya tsira bayan harin da sojin kawancen naton suka kai a ranar asabar da daddare akan gidan dan nasa wato saiful Arab.

Wannan hari dai na sojojin NATO yayi sanadiyyar rasuwar Saiful Arab Gaddafi da kuma wasu jikokin Kanal Gaddafin su uku a cewar rahotanin

Saif dai ya rasu yana da shekaru ashirin da tara a duniya.

Jami'an kasar libyan dai sun kwashi manema labarai zuwa gidan Saif, wanda yake a birnin Tripoli inda sojin kawancen Naton sukai aman wuta, harin dai yayi kacha kacha da gidan

Sai dai shugaba Gaddafin da matarsa na cikin koshin lafiya inji mai magana da yawunnasa

Ga alamu dai wannan shine hari da sojin kawancen Naton suka kai cikin sa'oi ashirin da hudu.

Rahotanni sunce wani makami mai linzamin ya sauka da sanyin safiyar asabar a kusa da gidan talabijin din kasar, a lokacin da shugaba Gaddafin yake jawabi, jawabin daya sake nanata cewar ba zai taba bada kai bori ya hau ba, amma yace a shirye suke su tsagaita wuta idan har dukkanin bangarorin biyu suka amince da yarjejeniyar hakan

Ya zuwa yanzu dai sojojin Naton basu ce komai ba dangane da wannan labari.

Sai dai sakataren fadar white house Jay carney yace fadar ta White House na sane da labarin mutuwar dan kanal Gaddafin amma yace suma suna bin diidigin labarin

A shekarar 1986 ne dai Kanal Gaddafin ya rasa wata 'yarsa bayan wani harin sama da sojin kasar Amurka suka kai a birnin Triplon

Rahotani dai sunce 'ya tawayen birnin Bengazi sunyi ta shagulgula ta hanyar yin harbe harben bindigogi cikin dare domin nuna farincikinsu game da labarin rasuwar Saiful Arab