Hari kan ofisoshin jakadanci a Libiya

Zanga zanga a Tripoli Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Zanga zanga a Tripoli

A Libiya, jama'a cike da fushi sun afkawa ofisoshin jakadanci a Tripoli, babban birnin kasar, bayan an bada labarin cewa, daya daga cikin 'ya'yan Kanar Gaddafi ya rasa ransa, a wani harin da kungiyar tsaron NATO ta kai.

An kone ofishin jakadancin Birtaniya kurmus, wanda hakan ya sa Birtaniyar ta kori jakadan Libiyar daga kasarta.

A nata bangaren, Majalisar Dinkin Duniya ta ce za ta kwashe ma'aikatanta, 'yan kasashen waje daga Tripolin, bayan da aka yiwa ofishohinta a birnin kakaf.

A yau gidan talabijin din gwamnatin Libiyar ya nuno wasu gawarwarkin mutane hudu, cikin likkafani, wadanda aka ce na Saif al-Arab ne, dan Kanar Gaddafi, da kuma na jikokin Kanar din su uku.

A cikin wata sanarwa a yau, Rasha ta nuna shakku game da ikirarin kasashen kawance, na cewa ba wai sun kafa kahon zuka ne akan Gaddafi da iyalansa ba.