An daukaka Paparoma John Paul na 2

Bikin daukaka Paparoma John Paul na 2 Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Bikin daukaka Paparoma John Paul na 2

An daukaka Paparoma John Paul na 2, a gaban masu ibadar da aka kiyasta sun zarta miliyan guda, a fadar Vatican.

Paparoma Benedict mai ci a yanzu, ya bayyana wanda ya gadan, dan kasar Poland, wanda ya rasu shekaru 6 da suka wuce, a matsayin wanda Allah ya daukaka a Cocin Roman Katolika.

Wannan shine mataki na karshe kafin zama Waliyi.

A wajen wata addu'a a dandalin St Peter, Paparoma Benedict ya yabawa John Paul na 2, kan yadda ya taimaka wajen sauya abinda ya kira: ka'idojin kwaminisancin da ba za a koma gare su ba, da kuma karfafawa mabiya a ko'ina cikin duniya gwiwar yin alfahari da addininsu na Krista.

Wannan ne taro mafi girma a birnin Rome, tun bayan jana'izar Paparoma John Paul na 2.