An kashe Osama bin Laden

Usama Bin laden da AymanAlzawahir da Muhammad Atef
Image caption Usama Bin laden da AymanAlzawahir da Muhammad Atef

Jami'an gwamantin Amurka sun ce, an kashe shugaban kungiyar Al-Qaeda, Usama bin Laden, kuma Amurka ta samu gawarsa.

Dakarun Amurka dai sun jima suna farautar Osama bin Laden, tun ma kafin harin sha daya ga watan Satumbar 2001, lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar kusan dubu uku.

Wakilin BBC ya ce: "A matsayinsa na wanda ya kafa kungiyar Al-Qaeda, kuma yake jagorantarta, Usama bin Laden ya kasance sananne a duniya, inda wasu a kasashen yammacin duniya ke kallonsa a matsayin tushen ta'ddanci.

Shugaba Obama wanda ya sanar da kashe Usama ya ce, kisan nasa ya biyo bayan fafatawar da aka yi ne, kuma tuni Amurka tana rike da gawar sa.

Ana zargin Usama da aikata manyan laifuka a sassa dabam-daban na duniya ciki har da harin sha daya ga Satumba da aka kai kan tagwayen gine-ginen cibiyar kasuwancin duniya dake New York a kasar Amurka.

Shi ne dai babban mutumin da Amurka ke nema ruwa a jallo.

Tuni dai kasar Amurka ta sanya ofisoshin jakadancinta a kasashen duniya cikin shirin ko ta kwana.

Mutane da dama ne suka taru a gaban fadar White House da ke Washington DC suna ta nanata kalmar "USA, USA" bayan an samu labarin mutuwar Usama.

Hari kan harabar gidan da yake ciki

Hakkin mallakar hoto GETTY IMAGES
Image caption Harin Sha daya ga Satumba

Shugaba Obama na Amurka ya ce an bashi labari a watan Agustan da ya gabata cewa akwai yiwuwar a samu bayanan inda Usama Bn Laden yake.

Yace a lokacin babu tabbaci, hakan ya sa suka shafe watanni suna bibiyar bayanai.

"Na gana a lokuta da dama da masu bani shawara kan al'amuran tsaro, kuma muka yi ta tattara bayanai a kan yiwuwar mun gano inda Bin Laden yake boye can cikin harabar wani gida dake can cikin kasar Pakistan. In ji shugaba Obama na Amurka.

Ya kuma kara da cewa: " Daga karshe a makon da ya gabata, na yanke cewa mun samu isassun bayanai da za su sanya mu dau mataki, don haka na bada umarnin a kamo Usama don hukunta shi.

Kuma ranar Lahadi, wasu dakarun kasar Amurka suka kai hari a Abbottabad kimanin kilomita dari arewa maso gabashin birnin Islamabad.

Bayan 'fafatawa' an kashe Bin Laden, kuma sojojin Amurka na rike da gawar sa, in ji shugaba Obama.

Jirgin Amurka daya dai ya rikito a lokacin harin.

An kashe wasu karin mutane uku a harin, ciki har da dan Usama bin Laden din da kuma wata mata yayinda aka ji wa wasu matan biyu rauni.

Usama

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mutane da dama na murnar kashe Usama a Amurka

Sunan Osama Bn Laden, mutumin da ya kafa kungiyar Al-Qaeda ya zama ruwan dare gama duniya, a cikin shekaru da dama.

A wajen mutanen da ke yammacin duniya, abin da yake fara zuwa a ransu idan an ambaci sunan Usama shi ne, ta'addanci, kasancewa ana yi masa kallon mutumin da ya dauki nauyin kai hare-haren ranar 11 ga watan Satumbar shekarar 2001.

A wajen wadansu kuwa, Usama cikakken musulmi ne, wanda ya kaddamar da jIhadi kan kasashen yammacin duniya.

Usama Bn Ladan, wanda mahaifinsa wani attajiri ne, mai kamfanonin gine-gine, ya girma cikin jin dadi.

Sai dai jim kadan bayan da tarayyar Soviet ta mamaye Afghanistan, sai Usama ya shiga kungiyar mujahideen da ke kasar, inda suka fafata da dakarun tarayyar Soviet din.

Kuma tun daga nan ne ya kafa kungiyar Al-Qaeda.

Bayan ya dawo Saudi Arabia ne dai, ya fara caccakar shugabanninta, wadanda ya ce sun kyale Amurka ta shiga kasar.

Ya ce sun yi hakan ne, da zummar ganin sun kawar da dakarun Saddam Hussain daga Kuwait.

A shekarar 1998 ne dai Usama Bn Laden ya ayyana yaki kan Amurka.

Kuma a shekarar ne dai, kusan duk manyan kasashen duniya suka amince cewa shi ne mutumin da ya bayar da umarnin kai hari a ofisosnhin Amurka da ke gabashin Afurka.

A shekarar 2000, kungiyarsa ta Alqaeda ta yi rugu-rugu da wani jirgin yakin Amurka, sannan daga bisani, kungiyar ta kai hare-hare a biranen New York da Washington, a shekarar 2001.

Kuma duk da dala miliyan 27 da Amurka ta sanar ga duk wanda ya taimaka aka kama shi, Usama Bn Ladan ya ci gaba da zulle mata, inda ya kasance a boye, a wadansu yankuna masu cike da tsaunuka dake kan iyakar Afghanisatan da Pakistan.

Martani

Shugabannin siyasa da sauran al'ummomin duniya na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu dangane da kashe jagoran kungiyar alka'ida Usama bin Laden.

Tsohon shugaban Amurka George Bush, ya ce wannan gagarumar nasara ce ga Amurka, ga mutanen da ke neman zaman lafiya a sassa dabam-daban na duniya, da ma wadanda suka rasa rayukansu a harin ran sha daya ga Satumba.

Shi ma tsohon shugaban Amurka Bill Clinton ya ce, wannan batu ne mai matukar muhimmanci ba wai ga iyalan da suka rasa wani nasu a harin sha daya ga Satumba ba, da ma sauran hare-haren da kungiyar Alqaeda ta kai, amma ga mutanen duniya baki daya wadanda suke son gina makoma ta zaman lafiya ga duniya.

Fira Ministan Burtaniya David Cameroon, ya ce labarin mutuwar Osama bin Laden za ta kawo saukin lamari ga al'ummar duniya.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Usama a cikin wani kogo a shekarar 1998

Fira Ministan Israela Benjamin Netanyahu, na da ra'ayin cewa, wannan gagarumar nasara ce da kuma 'yanci, da kuma tsari na kasashen da ke amfani da demokradiyya wajen yakar ta'addanci kafada-da-kafada.

Shi ma Fira ministan kasar Kenya Raila Odinga, ya shaida wa BBC cewa babbar nasara ce a yakin da ake yi da ta'addanci.

Shi ma Fira Ministan New Zealand John Key, cewa ya yi Osama shi ne ya yi sanadin mutuwar dubban mutane, ciki har da 'yan kasar New Zealand a sassan duniya.

A nata bangaren, ma'aikatar harkokin wajen India cewa ta yi, ya kamata duniya ta kara azama wajen karfafa hadin kanta a yaki da ta'addanci.

Shi kuwa wani mazaunin birnin New York na kasar Amurka Justin King a sakon da ya aike wa BBC cewa ya yi, labarin kisan Usama abu ne mai kyau, sai dai irin martanin da mutane ke mayarwa babu dadin ji, musamman tsalle da murnar da mutane ke yi a kewayen fadar White House ta Amurka.