Kisan Osama ba karshen ta'addanci ba

Dakin da aka kashe Osama Bin Laden Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Dakin da aka kashe Osama Bin Laden

Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillari Clinton, ta ce kisan mutumin da ya kirkiro alqaeda, wato Osama Bin Laden da dakarun Amurka na musamman su kai, wani ci gaba ne a yaki da ta'addanci, amma kuma har yanzu da sauran aiki.

Inda ta ce kada a manta cewa yaki domin hana alqaeda da mukarrabanta gudanar da ayyukan ta'addanci ba zai tsaya da mutuwar Bin Laden ba.

Jami'an Amurka sun ce dakarun sojinsu sun yi jana'izar Osama bin Laden kamar yadda addinin musulunci ya tanadar, kafin daga bisani su binne shi a teku.

An ambato jami'an na cewa gwajin kwayoyin halittar da akai masa sun tabbatar da Osaman ne.

Mrs Clinton ta ce kisan wani sako ne ga Taliban na cewa ba za su yi nasara kan Amurka da kawayenta ba. Tace Taliban na da zabin yin watsi da alqaeda ta rungumi turbar zaman lafiya.