Masar na son a kafa kasar Palasdinu

Taswirar Masar
Image caption Masar na son a kafa kasar Palasdinu

Ministan hulda da kasashen wajen Masar, Nabil al-Araby yayi kira ga Amurka ta goyi bayan kafa 'yantacciyar kasar Palasdinu.

Ministan ya kara da cewa, kamata yayi Amurka ta yi la'akari da sasantawar da aka yi tsakanin bangarorin Fatah da kuma na Hamas wajen yin kira ga Isra'ila ta tattauna da Palasdinawa.

Wannan mataki na gwamnatin Masar dai na nuni ne ga gagarumin sauyin manufofinta na hulda da kasashen waje.

A baya dai Masar na yin biyayya ne ga duk wani matsayin Amurka da Isra'ila akan irin wadannan batutuwa.