Shariar tsohon shugaban Nijar, Mamadou Tandja

Mamadou Tandja
Image caption Tandja na tsare tun watan Fabrairun bara

A jamhuriyar Niger, kotun daukaka kara ta Yamai ta wanke tsohon shugaban kasar Tandja Mamadou daga laifufukan da ake zarginsa da su tun bayan da aka kifar da gwamnatinsa a watan Fabrairun bara.

Sai dai a yayin da jama'a ke dakun fitowarsa Tandjan daga kurkuku, alkalin gwamnati ya ce hakan ba zai yiwu ba har sai kotun ta sake yin wani sabon zama domin duba sabuwar karar da ya shigar a kan Tandjan.

A cikin sabuwar karar dai, wadda aka shigar a 'yan makonnin da suka wuce, ana zargin tsohon shugaban ne da hannu a batun salwantar da wassu makudan kudade a ma'aikatar samar da takin zamani.

A ranar Talata mai zuwa ce dai ake sa ran kotun za ta yanke hukunci a kan wannan sharia.