Bin Laden: Pakistan ta amince da abun kunya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gidan da aka kashe Osama Bin Laden

Hukumar leken asiri ta Pakistan, ISI tace babban abin kunya ne ga jami'anta na abin da ke nuna cewa basu da masaniyar jagoran alqaeda, Osama Bin Laden na zaune a wani gida mai kasa da nisan kilo mita daya da makarantar sojoji ta Pakistan. A ranar lahadi ne dakarun sojin Amurka suka kashe Osama bin Laden a lokacin da suka kai hari a gidan da yake a garin Abbot-tabad.

Yanzu haka wani jami'in hukumar leken asirin ta Pakistan ya bada karin haske game da harin da ya kashe Osaman, inda ya ce baya ga dauke gawar bin Laden da dakarun Amurkan sukai, sun kuma yi awan gaba da wani mutum da ransa a lokacin da sukai kai harin.

A cewar jami'an hukumar leken asiri na kasar Pakistan, akwai kimanin mutane 17 zuwa 18 a cikin gidan lokaci da sojojin Amurka suka kai harin.

Jami'an hukumar leken asirin Pakistan `din sun kuma bayyana cewa sun tattara wasu muhimman takardu da suka samu a cikin gidan.

To sai dai kasar ta Pakistan na fuskantar kakkausar suka daga bangarori da dama na tayi bayanin dalilan daya sa hukumomin kasar suka kasa sanin inda Osaman ke boye.

Ministan kasashen wajen Pakistan Salman Bashir bayan wata ganawa da jakadan Amurka na musamman a kasashen Pakistan da Afghanistan Marc Grossman, ya `ki yace uffan game harin da sojojin Amurka suka kai a gidan da Osama bin Laden `din ke boye, sai dai ya jaddada cewa kasar Pakistan zata ci gaba da bada hadin kai a kokarin da ake yi na yaki da ta'addaci.