Zaman Majalisar Dattawan Najeriya

Harabar Majalisar Dattawan Najeriya
Image caption Harabar Majalisar Dattawan Najeriya

A Najeriya a yau Majalisar Dattawan kasar ta koma zamanta bayan hutun da ta yi na tsawon lokutan zabukan da aka gudanar a kasar.

Sai dai sabanin hasashen da aka yi cewa za ta tattauna batun kasafin kudin kasa, Majalisar ta yi wani zama a kebe, wanda bayansa ta bayyana cewa matakin da hukumar zabe, INEC ta dauka a Jihar Imo da ke kudu maso gabashin kasar ya saba doka.

Hukumar zaben dai ta dakatar da bayyana sakamakon zaben gwamnan Jihar Imo tana mai cewa sai an sake zabe a kananan hukumomi guda hudu.