Uganda: Tattaunawa da jam'iyyun adawa ta wargaje

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption 'Yan sanda na tsare da shugabanin 'yan adawa a Uganda Kizza Besigye

Bayan shafe makwannin ana tashe tashen hankula a Uganda, kokarin tattaunawa tsakanin gwamnati da jam'iyyun adawa ta ci tura.

Babbar jam'iyyar adawa bata halarci taron ba tana mai cewa kamata yai mai shiga tsakani ya kasance mai zaman kansa ne.

Gwamnati ta haramta zanga zangar baya-bayannan da akai tayi, inda akai ta aranggama da 'yan sanda da sojoji.

Yanzu haka babban jagoran 'yan adawa, Doctor Kizza Besigye na kasar Kenya inda yake jinyar raunukan da aka ji masa a lokacin tashe tashen hankulan.

Kusan za'a iya cewa a bayyana take game da bukatar tattaunawa tsakanin gwamnati da 'yan adawa don kaucewa ci gaba da zubar da jini a titunan Uganda.

Sai dai babbar Jam'iyar adawa ta Forum For Democratic Change FDC, ta `ki halartar ganawar da aka shirya yi a birnin Kampala wanda babban Jami'in Jam'iyar dake mulki zai jagoranta.

Ita dai jam'iyar adawa ta FDC na son mai shiga tsakani ne da bai da alaka da kowane bangare ne, idan da hali ma ya kasance ya fito daga wata kasa.

Ta kuma yi kira ga shugaba Yoweri Museveni da ya nemi gafara dangane da yadda aka kame Doctor Kizza Besigye da `karfin tsiya a wata zanga zanga.

Su dai Mutanen biyu wato shugaba Yoweri Museveni da Doctor Kizza Besigye a baya abokan juna ne.

Shugaba Museveni ya kasance akan karagar mulki ne na tsawon shekaru 25, inda ya kada Doctor Besigye har sau uku a zabubbukan da ake takaddama akai.

'Yan adawa na kallon shugaba Museveni ne a matsayin mai mulkin kama karya inda suka ce an yi amfani da `karfin soji wajen farma masu zanga.

Da yake amsa tambaya ta gidan talbijin `din kasar akan yadda zai tunkari dokar ta baci a Uganda, shugaba Museveni ya bayyana cewa:

"Ina ganin Uganda watakila ta kasance kasar da tafi kowace kasa a duniya bin tsarin mulkin demukradiya, idan da za'a ce in gabatar da Lekca akan demukradiya, ina ganin ina da isasshen kwarewa akan haka."

Yanzu dai za'a iya cewa akwai gagarumin bambamci tsakanin ra'ayin shugaban kasar dana 'yan adawa, kuma duk wani yunkuri na sasantawa ka iya kasancewa da kamar wuya.