Lauyoyi za su yi bore a Uganda

Shugaban jam'iyar adawa, Kizza Besigye Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Lauyoyi za su yi bore a Uganda

A yau Laraba ne lauyoyin kasar Uganda za su yi wani zaman nuna bore a wata babbar kotu da ke birnin Kampala.

Za su yi boren ne saboda abin da suka kira, yin amfani da karfin da ya wuce kima da gwamnatin kasar ke yi.

A cikin wannan watan dai jami'an tsaro kasar sun harbe da kuma raunata mutane da dama a kokarin tarwatsa zanga-zangar nuna rashin amince da tsadar rayuwa.

Babbar jam'iyyar adawar kasar mai suna Forum for Democratic Change ce ta shirya zanga-zangar.

Yanzu haka dai shugaban jam'iyyar adawar, Kizza Besigye yana kasar Kenya inda ya ke jinyar raunukan da ya samu bayan kamun da jami'an tsaro suka yi masa.